logo

HAUSA

Sin za ta ci gaba da raya huldar dake tsakaninta da Switzerland

2024-01-16 10:18:00 CMG HAUSA

 

Firaministan Sin Li Qiang wanda yake ziyara a kasar Switzerland ya bayyana cewa, kasar Sin tana son ci gaba da raya dangantakar dake tsakaninta da Switzerland, domin kara amfana da hadin gwiwar moriyar juna.

Li ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da shugabar tarayyar Switzerland Viola Amherd, ganawar da ta samu halartar dan majalisar gudanarwa, Guy Parmelin, da shugaban ma'aikatar harkokin tattalin arziki, ilimi da bincike.

Tun bayan kulla huldar diflomasiya tsakanin kasashen biyu yau shekaru 74 da suka gabata, dangantakar dake tsakaninsu ta samu babban ci gaba, kuma ta kafa abubuwa na tarihi.

Li ya tunata da cewa, a shekarar 2016, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Switzerland, sun sanar da kulla huldar kirkire-kirkire bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Switzerland, wanda ya ba da muhimmin jagoranci wajen raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Firaministan ya ce, a shirye Sin take ta yi aiki tare da Switzerland, don aiwatar da muhimman ra'ayoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kara karfafa tushen amincewa da juna a fannin siyasa, da ci gaba da aikin hadin gwiwa na daidaito, kirkire-kirkire, da samun moriyar juna. (Ibrahim Yaya)