logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sin: Manufar kasancewar kasar Sin daya tak babban fata ne na al’umma

2024-01-16 20:17:15 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning, ta amsa tambayar da aka yi mata game da katse “huldar jakadanci” da kasar Nauru ta yi da yankin Taiwan, inda ta ce, kudurin gwamnatin Nauru na farfado da alakar jakadanci da kasar Sin ya sake shaida cewa, manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, babban fata ne na al’umma.

Gwamnatin kasar Nauru ta sanar a jiya Litinin cewa, ta yanke “huldar jakadanci” da hukumar yankin Taiwan, tare da bayyana fatan maido da huldar jakadanci da kasar Sin. Game da wannan batu, majalisar gudanarwa ta kasar Amurka ta fitar da sanarwa ta kafar intanet tana mai cewa, abun da Nauru ta yi, abu ne na rashin jin dadi, kuma Amurka za ta ci gaba da fadada mu’amala da Taiwan, da goya mata baya wajen kara shiga harkokin duniya.

Rahotannin da aka ruwaito sun kuma ce, majalisar wakilan Amurka ta zartas da wani shirin doka mai taken “kauce wa nuna bambanci ga Taiwan”, inda aka bukaci sakatariyar baitulmalin Amurka da ta goyi bayan shigar da Taiwan cikin asusun bada lamuni na duniya wato IMF, ta hanyar amfani da rawar da kasar ke takawa a asusun. Game da wannan batu, Mao Ning ta ce, wannan shirin dokar, tsoma baki ne da Amurka ta yi cikin harkokin gidan kasar Sin, kuma kasar Sin tana matukar adawa gami da nuna takaici ga wannan abu dake yunkurin wasa da siyasa bisa hujjar batun Taiwan.

Mao ta jaddada cewa, Taiwan ba ta da wata hujja ko dalili ko hakki, da ta cancanci shiga cikin Majalisar Dinkin Duniya da sauran wasu kungiyoyin kasa da kasa, inda wata kasa mai cikakken mulkin kai za ta iya shiga ciki. (Murtala Zhang)