logo

HAUSA

Kasar Sin na sa ran samun adadin tafiye-tafiyen biliyan 9 a lokacin bikin bazara

2024-01-16 21:32:55 CMG Hausa

Ma’aikatar kula da harkokin sufuri ta kasar Sin, ta ce ana sa ran samun tafiye tafiye da yawansu ya kai biliyan 9, adadin da zai kai matsayin koli, yayin lokacin hutun bikin bazara, wato bikin sabuwar shekara na al’ummar kasar.

Lokacin tafiye-tafiyen, wanda ake samun karuwar bukatar ababen sufuri yayin da mutane ke komawa gida domin haduwa da iyalansu, zai fara ne daga ranar 26 ga watan Junairu zuwa 5 ga watan Maris na bana.

Yayin wani taron manema labarai a yau Talata, mataimakin ministan ma’aikatar, Li Yang, ya bayyana cewa, ana sa ran tafiye-tafiyen fasinjoji ta jiragen kasa da na sama da na ruwa da motoci, zai kai biliyan 1.8 a lokacin.

A cewar Li Yang, kaso 80 na tafiye tafiyen za su kasance na tukin mota da mutane za su yi da kansu, adadin da ake ganin ka iya kai wa wani sabon matsayi. (Fa’iza Mustapha)