logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Tunisiya

2024-01-16 10:51:16 CMG Hausa

Jiya Litinin, mamban ofishin siyasar kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Tunisiya Nabil Ammar a birnin Tunisiya, fadar mulkin kasar Tunisiya.

Wang Yi ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi mu’amala da kasar Tunisiya wajen inganta fasahohin gudanawar harkokin kasa, kuma tana goyon bayan kasar Tunisiya wajen kara karfinta na neman bunkasuwa cikin ‘yancin kai, domin samun ci gaba da wadata cikin hadin gwiwa.

A nasa bangare kuma, minista Ammar ya ce, kasarsa tana mai da matukar hankali wajen zurfafa zumuncin dake tsakanin kasashen biyu, kuma, tana godiya ga kasar Sin dangane da taimako da goyon bayan da ta nuna mata. Kasar Tunisiya tana fatan yin hadin gwiwa da kasar Sin wajen inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)