logo

HAUSA

Shugaban kasar Masar da ministan harkokin wajen kasar Sin sun tattauna kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da rikicin Gaza

2024-01-15 11:28:13 CMG Hausa

Shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi wanda ke ziyara a kasar sun gana a jiya Lahadi, inda bangarorin biyu suka tattauna kan yadda za a karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, tare da jadadda muhimmancin aiwatar da tsagaita wuta a zirin Gaza.

Da farko dai Wang ya mika sakon gaisuwar shugaban kasar Sin Xi jinping ga shugaba Sisi. Inda ya bayyana cewa akwai zumunci mai karfi tsakanin Xi da Sisi, wanda shi ne “tabbacin karfin dangantakar dake tsakanin Sin da Masar”.

Wang ya kuma taya Sisi murnar sake zabarsa da aka yi, yana mai bayyana yakinin cewa Masar za ta cimma sabbin nasarori masu girma a kan yunkurinta na tabbatar da ci gaban kasa da sake farfado da kasa.

A nasa bangare, Sisi ya taya kasar Sin murna kan manyan nasarorin da ta samu a karkashin jagorancin shugaba Xi da kuma rawar da take takawa a harkokin kasa da kasa.

Dangane da rikicin da Isra’ila da Falasdinu ke ci gaba da yi a zirin Gaza, bangarorin biyu sun amince da cewa, ya kamata a gaggauta tsagaita bude wuta da kuma kawo karshen tashin hankalin, don hana shi ci gaba da yaduwa. (Muhammed Yahaya)