logo

HAUSA

Ministocin harkokin wajen kasashen Sin da Masar sun cimma matsaya mai muhimmaci yayin tattaunawa a birnin Alkahira

2024-01-15 10:21:53 CMG Hausa

A jiya Lahadi ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa, a cikin shekaru goma da suka gabata, tun bayan da aka kulla dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Masar, kasashen biyu sun bude wani kyakkyawar babi na samun ci gaba a dangantakar dake tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare a karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu. 

Wang, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da suka gudanar tare bayan tattaunawa da ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry a birnin Alkahira na kasar Masar.

Ministocin biyu sun yi tattaunawa mai inganci tare da cimma matsaya da dama, a cewar Wang.

Da farko dai, kasashen biyu za su ci gaba da zurfafa amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare tare da tabbatar da goyon bayan juna wajen kiyaye muhimman muradu.

Na biyu kuma, kasashen biyu za su yi aiki tare wajen samar da ingantacciyar hanyar gina shawarar ziri daya da hanya daya don cimma moriyar juna da samun nasara a babban mataki.

Na uku, ya zama wajibi a karfafa tattaunawa ta zamani tsakanin juna da kara zurfafa mu'amala tsakanin bangarorin biyu.

Na hudu, akwai bukatar kasashen biyu su kara yin cudanya da hadin gwiwa kan batutuwan da suka shafi shiyya-shiyya da na kasa da kasa.

Ministan harkokin wajen kasar Sin ya sake taya kasar Masar murnar zama sabuwar mamba a kungiyar BRICS, inda ya bayyana aniyar kasar Sin na yin aiki tare da kasar Masar wajen karfafa hadin gwiwar kasashen BRICS, da sa kaimi ga gudanar da harkokin duniya baki daya, wajen samar da daidaito da kuma tsari a duniya, da sa kaimi ga hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu da dunkulewar tattalin arziki da zai amfanar da kowa. (Muhammed Yahaya)