logo

HAUSA

CMG ta kammala bitar farko ta shagalin murnar Bikin Bazara na bana

2024-01-15 21:49:04 CMG Hausa

Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ya gudanar da bitar farko ta shagalin murnar shiga sabuwar shekarar gargajiya ta al’ummar kasar Sin na bana, inda aka gabatar da wasanni iri-iri, dake kunshe da kade-kade da raye-raye, da wasannin kwaikwayo na gargajiya, da wasannin barkwanci da makamantansu. Kana, an kirkiro sabbin fasahohin zamani don gabatar da shagalin.

CMG din za ta gabatar da wani kayataccen shagalin murnar shiga sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin, mai kunshe da sabbin kirkire-kirkire, da wasanni masu ban sha’awa, don nishadantar da miliyoyin masu kallo, a jajibirin sabuwar shekara. (Murtala Zhang)