logo

HAUSA

Sin na kafa sabon tarihi

2024-01-15 09:30:21 CMG HAUSA

Bayan Thomas Bach ya zama shugaban kungiyar Olympics ta duniya a shekarar 2013, ya mai da kasar Sin zangon farko na ziyararsa. A wannan shekara kuma, Sin ta gabatar da rokon daukar bakuncin shirya gasar Olympics ta lokacin hunturu a shekarar 2022.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, burin neman daukar bakuncin gasar shi ne ingiza mutane da yawansu ya kai miliyan 300 shiga wasan kankara.

Bayan shekaru biyu kuma, wasan kankara ya shahara matuka a nan kasar Sin. Thomas Bach na ganin cewa, gasar da Sin ta shirya ta zama wani muhimmin batu ga wasan hunturu, wato daga wannan lokaci, wasan kankara ya kara samun karbuwa a duniya. Bach na matukar godiya da taimakon da shugaba Xi da kasarsa suka baiwa gasar. Ya ce, idan Sin ta tsai da wani buri, ba shakka za ta yi iyakacin kokarin tabbatar da shi, wannan dalilin da ya sa Beijing ya kafa sabon tarihi yanzu.