logo

HAUSA

A shirye Sin take ta hada kai da Switzerland wajen tinkarar kalubalen duniya tare

2024-01-15 11:38:20 CMG Hausa

Firaministan Sin Li Qiang ya bayyana cewa, a ko da yaushe kasar Sin tana mai da hankali sosai kan rawar da Switzerland take takawa a nahiyar Turai, da ma fagen kasa da kasa, kuma a shirye take ta ci gaba da yin cudanya da hadin gwiwa da Switzerland, wajen tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta.

Li ya bayyana hakan ne, a wurin taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya (WEF) na shekarar 2024 da kuma ziyarar aiki a kasar ta nahiyar Turai. Inda ya samu tarba daga shugabar tarayyar Switzerland Viola Amherd a filin jirgin saman kasa da kasa na Zurich.

Li ya kara da cewa, Switzerland na daya daga cikin kasashen yammacin duniya, da suka kulla huldar diflomasiyya da kasar Sin, kuma huldar da kasashen biyu suka kulla shekaru 74 da suka gabata, ta samu ci gaba mai inganci.

Li bayyana cewa, a shirye Sin take ta yi aiki tare da Switzerland, wajen martaba muhimman tsare-tsare da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kara amincewa da juna a fannin siyasa, da fadada hadin gwiwar moriyar juna, da kulla zumunci tsakanin jama'ar kasashen biyu.(Ibrahim)