logo

HAUSA

Kasar Sin na adawa da tsokacin Amurka kan zaben yankin Taiwan

2024-01-14 21:45:17 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bukaci Amurka ta dakatar da duk wata mu’amala a hukumance da yankin Taiwan, kuma ta daina aikewa da mummunan sako ga masu neman ballewar yankin.

Kasar Sin ta yi wannan kira ne a yau Lahadi, biyo bayan sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar game da zaben da aka gudanar a yankin Taiwan na kasar Sin.

Cikin sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Sin ta fitar, Sin ta bukaci Amurka ta kiyaye ka’idar kasar Sin daya tak da kuma sanarwoyin hadin gwiwa uku dake tsakanin Sin da Amurka, tare da yin abubuwan da suka dace da alkawurran da shugabannin kasar suka sha nanatawa dake cewa ba sa goyon bayan ‘yancin kan Taiwan, ko kasashen Sin biyu, ko Taiwan daban, Sin daban. Har ila yau, sanarwar ta bukaci Amurka ta daina amfani da batun yankin na Taiwan a matsayin wani makami na dakile ci gaban kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)