logo

HAUSA

Ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Sin sun yi tsokaci kan sakamakon zabukan Taiwan

2024-01-14 16:43:22 CMG Hausa

Mai magana da yawun ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, Chen Binhua, ya yi bayani kan sakamakon zaben yankin Taiwan da yammacin jiya 13 ga wata, inda ya ce, sakamakon zabukan biyu a Taiwan ya shaida cewa, jam’iyyar Democratic Progressive Party wato DPP ba ta iya wakiltar muradun jama’ar yankin. Ya ce Taiwan, yanki ne da ba za’a iya ware shi daga kasar Sin ba, kuma zaben ba zai iya sauya babban tushe gami da alkiblar dangantakar Taiwan da babban yankin kasar Sin ba, kana ba zai iya sauya babban fatan al’ummomin bangarorin biyu na kara yin mu’amala da kusantar juna ba, kuma ba zai iya sauya makomarsu ba, wato tabbas za a samu dunkulewar kasar Sin baki daya.

A nasa bangare, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, harkokin Taiwan, harkokin siyasa ne na cikin gidan kasar Sin. Ya ce ba tare da la’akari da sauyawar halin da ake ciki a wurin ba, kasar Sin za ta kasance daya tak a duniya, kuma Taiwan wani yanki ne na kasar, lamarin da ba za’a iya sauyawa ba. Ya ce gwamnatin kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan manufar kasantuwar kasarta daya tak a duniya, da nuna adawa da masu yunkurin balle Taiwan daga babban yankin kasar, da nuna adawa da “kasancewar Sin guda biyu” da “Sin daban, Taiwan daban”, kuma ba za ta sauya wannan matsayi ba. Bugu da kari, kasa da kasa suna tsayawa kan ra’ayi daya na kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kuma hakan ba zai sauya ba.

An yi zabukan jagoran yankin Taiwan gami da wakilan jama’ar yankin na bana a jiya Asabar, inda sakamakon zabukan ya nuna cewa, ‘yan takarar dake karkashin tutar jam’iyyar DPP, Lai Ching-te da Hsiao Bi-khim sun zama jagora gami da mataimakiya. A cikin kujeru 113 na majalisar kafa dokokin yankin Taiwan kuma, jam’iyyar Chinese Kuomintang party ta samu guda 52, yayin da jam’iyyar DPP ta samu 51, kana jam’iyyar TPP ta samu guda 8, sai kuma ‘yan takara indipenda suka samu 2. (Murtala Zhang)