logo

HAUSA

Liu Jianchao ya ziyarci kasar Amurka

2024-01-14 17:20:07 CMG Hausa

Daga ranar 8 zuwa 13 ga wata, shugaban sashen tuntubar kasashen waje na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, Liu Jianchao, ya shugabanci tawagar ‘yan jam’iyyar, don ziyartar kasar Amurka, inda ya yi shawarwari da mutanen kasar da dama, ciki har da sakataren harkokin wajen kasar, Antony Blinken, da babban mataimakin mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin tsaro, Jon Finer, da ‘yan majalisun dattawa da wakilai na jam’iyyun kasar biyu wato Democratic Party da Republican Party, da magajin garin San Francisco London Breed, gami da mutane daga bangarorin kudi da masana’antu da kasuwanci da ilimi da kafafen yada labarai da sauransu, tare da halartar taron karawa juna sani karkashin shawarwarin Sin da Amurka da ake kira China-U.S. Track 1.5 Dialogue, da kuma gabatar da jawabi a wajen taron kwamitin kula da harkokin waje na Amurka. Jami’in ya kuma gana da sakatare-janar na Majliasar Dinkin Duniya, Antonio Guterres.

Tawagarsa ta kuma yi musanyar ra’ayoyi tare da bangarorin Amurka, dangane da makomar ci gaban kasar Sin, da alakar Sin da Amurka, da daidaita harkokin duniya da sauransu.

Kasashen Sin da Amurka sun kuma ce, za su ci gaba da tabbatar da muhimman ra’ayoyi iri daya da shugabanninsu Xi Jinping da Joe Biden suka cimma, da daukar matakan zahiri, a wani kokari na ciyar da dangantakarsu gaba cikin dogon lokaci kuma ta hanyar da ta dace. (Murtala Zhang)