logo

HAUSA

Cinikin waje na kasar Sin ya karu da 0.2% a shekarar 2023

2024-01-12 15:29:44 CMG Hausa

Jimillar kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su da kuma fitar da su ya karu da kashi 0.2 cikin dari a shekarar 2023 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a shekarar 2022, kamar yadda kididdiga ta nuna a hukumance.

A shekarar 2023, cinikin waje na kasar ya kai yuan tiriliyan 41.76 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 5.87, a cewar hukumar kwastam ta kasa (GAC).

Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, yawan kayayyakin da aka fitar zuwa kasashen waje ya karu da kashi 0.6 cikin dari wanda ya kai yuan tiriliyan 23.77 a shekarar 2023 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a shekarar 2022, yayin da kayayyakin da ake shigowa da su daga ketare suka ragu da kashi 0.3 cikin dari daga shekarar da ta gabata zuwa yuan triliyan 17.99.

Bayanai sun nuna cewa har yanzu kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa zuwa kasashen waje suna kan gaba a kasuwanni idan aka kwatanta da na sauran kasashen, a cewar mataimakin shugaban GAC Wang Lingjun a taron manema labarai. (Muhammed Yahaya)