logo

HAUSA

Manzon musamman na shugaban Sin zai halarci taron koli karo na 19 na kungiyar kasashe 'yan ba-ruwanmu

2024-01-12 20:37:11 CMG HAUSA

 

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta sanar a gun taron manema labarai a yau cewa, manzon musamman na shugaban kasar Sin kana mataimakin firaministan kasar Sin Liu Guozhong, zai halarci taron koli karo na 19 na kungiyar kasashe 'yan ba-ruwanmu da taron shugabannin kasashe masu tasowa karo na 3 bisa gayyatar da aka yi masa daga ran 15 zuwa 24 ga watan nan a Uganda. Bayan taron, zai kai ziyarar aiki kasashen Aljeriya da Kamaru da Tanzaniya.

Game da matakan da Amurka ke dauka da suka shafi yankin tekun Indiya da Pasifik kuwa, Mao Ning ta ce, dole ne Amurka ta mutunta moriyoyin kasashen yankin, da kara yin abubuwan da za su taimaka wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, ba ta bullo da rikicin kungiyanci ko jefa yankin cikin rikici ba.

Yayin da take magana kan batun Taiwan na kasar Sin, Mao Ning ta ce, kasar Sin na fatan Amurka za ta mutunta alkawuran da ta dauka, da daidaita al'amurran da suka shafi yankin Taiwan cikin tsanaki yadda ya kamata, da kuma daina aika duk wani mummunan sako ga 'yan aware na Taiwan.

A wani taron manema labarai, kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin, KanarZhang Xiaogang ya bayyana cewa, tushen matsalar tsaron ruwa da sama na sojan kasar Sin da Amurka, shi ne yadda jiragen ruwa da na sama na Amurka suka zo yankin kasar Sin don haifar da matsala, da kuma tsokana. Abin da ya kamata Amurka ta yi shi ne, ta dakatar da duk wasu ayyuka masu hadari da tsokana tare da takaita ayyukan sojojinta. Ya kuma ce, kasar Sin tana son yin mu’amala da hadin gwiwa da sojojin Amurka bisa daidaito da mutuntawa. (Amina Xu)