logo

HAUSA

Bude kofar kasar Sin: Sabbin matakan shige da fice da aka bullo da su don saukaka wa baki shiga kasar Sin

2024-01-12 10:55:40 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Sin ta sanar da sabbin matakai na saukaka balaguro zuwa kasar Sin ga 'yan kasashen waje.

Hukumar kula da shige da fice ta kasar Sin ta sanar da sabbin matakai guda biyar a ranar Alhamis, tare da aiwatar da matakan nan da nan don saukaka balaguro zuwa kasar Sin.

Matakan sun hada da saukaka yanayin neman biza ga wasu ’yan kasashen waje dake neman bizar tashar jiragen ruwa don shiga kasar Sin. Misali, wadanda ke bukatar yin tafiya cikin gaggawa zuwa kasar Sin za su iya ta hanyar gabatar da wasikun gayyata ko wasu takardu masu nasaba ga hukumomin shiga tashar. ’Yan kasashen waje dake tafiya zuwa wata kasa na iya yada zango a kasar Sin cikin sa'o'i 24 ta daya daga cikin filayen tashi da saukar jiragen sama 9 da suka hada da filin jirgin sama na kasa da kasa na Beijing, ba tare da bin ka'idojin binciken kan iyaka ba, an samar da wurare da ke kusa fiye da wuraren da aka amince da su a baya don neman karin kwanakin biza, da sake ba bayar wa ko canzawa ga ’yan kasashen waje da ke zama a kasar Sin. ’Yan kasashen waje dake bukatar shiga da fita kasar Sin sau da yawa za su iya neman bizar shiga na sau da daya. Kuma an saukaka bukatun takardun neman biza.

Mataimakin daraktan hukumar kula da shige da fice ta kasar Liu Haitao ya ce, "Yayin da tattalin arzikin kasar Sin ke ci gaba da farfadowa da kuma ingantuwa, kuma ake ci gaba da fadada matakan bude kofa ga waje, kamfanoni da jama'ar kasar Sin da na kasashen waje suna da sabbin bukatu da dama na kula da harkokin shige da fice. Hukumar NIA za ta hada kai da hukumomin da abin ya shafa, don saukaka wa baki da ke zuwa kasar Sin yin kasuwanci, karatu, da tafiye-tafiye." (Muhammed Yahaya)