logo

HAUSA

Sin da Amurka sun kaddamar da rukunin aiki kan sauyin yanayi

2024-01-12 19:21:46 CMG Hausa

A yau ne, kasashen Sin da Amurka suka fara gudanar da aikin rukuninsu kan matakan yaki da sauyin yanayin a shekarun 2020 ta kafar bidiyo.

An kaddamar da rukunin aiki ne, domin aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma a taronsu na San Francisco, da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, domin tunkarar matsalar sauyin yanayi.

A cewar ma'aikatar kula da muhalli ta kasar Sin, bangarorin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi kan fara aikin kungiyar cikin nasara, da zurfafa da gudanar da tattaunawar abokantaka kan muhimman fannonin hadin gwiwa, da suka hada da batun sauya salon amfani da wutar lantarki, da makamashin methane, da samarwa da amfani da kayayyaki, da larduna da jihohi da biranen da suke rage fitar da iskar carbon. (Ibrahim)