logo

HAUSA

Yawan saye da samarwa na motocin kasar Sin ya zarce miliyan 30

2024-01-11 16:34:39 CMG Hausa

Bisa kididdigar da kungiyar masana’antun kera motoci ta kasar Sin ta bayar a yau Alhamis, a shekarar bara, yawan saye da samarwa na motocin kasar Sin ya zarce miliyan 30, wanda ya kai sabon matsayi a cikin tarihi.

Daga cikinsu, an fitar da motoci miliyan 4.91 zuwa kasashen ketare, kuma ana sa ran kasar za ta zama kasar da ta fi fitar da motoci a duniya. (Safiyah Ma)