logo

HAUSA

Ministan kasuwancin Sin ya tattauna da takwaransa ta Amurka ta wayar tarho

2024-01-11 19:00:14 CMG Hausa

Ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin ta sanar Alhamis din nan cewa, ministan harkokin ciniki na kasar Sin Wang Wentao, ya tattauna ta wayar tarho da sakatariyar kasuwancin Amurka Gina Raimondo.

Bangarorin biyu sun gudanar da tattaunawa mai zurfi bisa manyan tsare-tsare a kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya, tare da mai da hankali kan aiwatar da muhimman matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma a taron birnin San Francisco na kasar Amurka.

Wang ya ce, taron na San Francisco ya nuna alkiblar ci gaban hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayha tsakanin kasashen Sin da Amurka, kana ya kamata matakan tattaunawa tsakanin sassan kasuwancin kasashen biyu, su taka rawar gani wajen samar da yanayi mai kyau na hadin gwiwar kasuwanci.

Ya kuma bayyana matukar damuwa, game da takunkumin da Amurka ta sanya kan fitar da na'urorin lithography da wasu kamfanoni ke yi zuwa kasar Sin, da bincike kan tsarin samar da sassan na'urorin laturori, da kakaba takunkumi da neman dakile ci gaban kamfanonin kasar Sin. (Ibrahim)