logo

HAUSA

Yakin Sudan ya haifar da matsalar gudun hijira mafi girma a duniya

2024-01-11 13:55:40 CMG Hausa

Ofishin kula da agajin jin kai na MDD (OCHA), ya ce yaki tsakanin dakaru a Sudan ya haifar da adadi mafi yawa na ‘yan gudun hijira a duniya, tare da kawo cikas ga yakin da ake da barkewar cutar amai da gudawa.

Ofishin ya bayyana a jiya Laraba cewa, tun daga watan Afrilun bara, sama da mutane miliyan 6 sun rasa matsugunansu a cikin kasar, ciki har da wasu sama da 500,000 da suka rasa matsugunansu sanadiyyar rikicin da ya barke a jihar Aj Jazirah a watan da ya gabata. A cewar ofishin, sama da wasu miliyan 1.3 sun tsallaka iyakokin kasar, inda suke gudun hijira a kasashe makwabta kamar Chadi da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da Masar da Habasha da Sudan ta Kudu.

Ofishin ya kuma bayyana damuwa da yadda rikicin ke yin tsaiko ga ayyukan jin kai, ciki har da yakin da ake da barkewar cutar amai da gudawa dake tsananta.

Hukumar lafiya ta duniya da ma’aikatar lafiya ta Sudan, sun bada rahoton dake zargin kusan mutane 9,000 sun kamu da cutar, ciki har da 245 da suka mutu a jihohi 9, adadin da ya karu da kaso 40 idan aka kwatanta da wanda aka samu wata guda da ya gabata. (Fa’iza Mustapha)