logo

HAUSA

Wang Yi ya tattauna ta wayar tarho da ministan wajen Rasha Sergey Lavrov

2024-01-11 12:00:33 CMG Hausa

Mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kana ministan wajen Sin Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho da ministan wajen Rasha Sergey Lavrov, inda suka nuna gaisuwar murnar sabuwar shekara ga juna.

Wang Yi ya bayyana cewa, a bana ake cika shekaru 75 da kulla dangantakar diplomassiya tsakanin Sin da Rasha, kuma a bana aka bude shekarar nune-nunen al’adun kasashen biyu. Ya ce ya kamata bangarorin biyu su bi matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, su gudanar da bikin murna, da karfafa mu’ammala tsakanin manyan jami’ai, da inganta ci gaban hadin gwiwa mai inganci na bangarorin biyu, da inganta mu’ammalar al’adu a fannoni daban daban, ta yadda za a karfafa tushen dangantakar al’ummun kasashen biyu.

A nasa bangare, Lavrov ya bayyana cewa, dangantakar Rasha da Sin ta samu babban sakamako a shekarar 2023. Kuma a cikin sabuwar shekara, bangaren Rasha yana fatan gudanar da mu’ammala tsakanin manyan jami’ai tare da bangaren Sin, da karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da zuba jari da sauransu, da karfafa mu’ammala a kan fanonin motsa jiki da al’adu da sauransu, da gudanar da shekarar nune-nunen al’adun Rasha da Sin, da karfafa mu’ammalar bangarorin biyu a kan harkokin kasa da kasa, da inganta dangantakar kasashen biyu ta yadda za a samu sabon sakamako. Har ila yau, ya ce Rasha na tsayawa tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak a ko da yaushe.

Ban da wannan kuma, bangarorin biyu sun yi musayar ra’ayi a kan hadin gwiwar kungiyar BRICS da rikicin Falasdinu da Isra’ila. (Safiyah Ma)