logo

HAUSA

Firaministan Sin zai halarci taron shekara-shekara na WEF da kai ziyara Switzerland da Ireland

2024-01-11 20:31:56 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Mao Ning, ta sanar a yau Alhamis cewa, firaministan kasar Sin Li Qiang, zai halarci taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya (WEF) na shekarar 2024, kana zai kai ziyarar aiki a kasashen Switzerland da Ireland daga ranar 14 zuwa 17 ga wata.

Mao ta tara da cewa, Li zai kai ziyarar ce bisa gayyatar Klaus Schwab, wanda ya kafa kuma shugaban zartarwa na WEF, da shugaban tarayyar Switzerland Viola Amherd, da kuma firaministan Ireland, Leo Varadkar. (Ibrahim)