logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping da takwaransa na Tunisia sun taya juna murnar cika shekaru 60 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashensu

2024-01-10 11:46:22 CMG Hausa

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Tunisia Kais Saied suka mikawa juna sakon murnar cika shekaru 60 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashensu.

A cikin sakonsa, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, Sin da Tunisia sun sada zumunta da juna mai zurfi. Kuma Sin tana bayar da muhimmanci sosai ga raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Tunisia, inda ya ce yana son hada hannu da shugaba Saied wajen amfani da damar cika shekaru 60 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashensu domin ci gaba da sada zumunta da juna, da sa kaimi ga raya hadin gwiwarsu zuwa wani sabon matsayi.

A nasa bangare, shugaba Saied ya bayyana cewa, Tunisia da Sin sun dade suna sada zumunta a tsakaninsu, da samun nasarori da dama karkashin hadin gwiwarsu. Ya ce kasar Tunisia tana son hada hannu da kasar Sin wajen raya sabuwar dangantakar abokantaka dake shafar fannoni daban daban wanda kuma ke da kyakkyawar makoma, ta yadda za a inganta dangantakar kasashen biyu zuwa sabon matsayi.

A wannan rana, shi ma firaminstan kasar Sin Li Qiang ya mika sakon murna ga takwaransa na kasar Tunisia Ahmed Hachani. (Zainab Zhang)