logo

HAUSA

An shirya harba na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-6 ta kasar Sin a rabin farko na shekarar 2024

2024-01-10 15:55:57 CMG Hausa

Hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin ta bayyana a yau Laraba cewa, an tsara harba na’urar Chang’e-6 ta kasar Sin mai binciken duniyar wata, a rabin farko na bana.

A cewar hukumar, tuni aka kai kayayyakin na’urar Chang’e-6 zuwa cibiyar harba kumbuna ta Wenchang dake lardin Hainan na kudancin kasar Sin. Kuma za a gudanar da gwaje-gwaje kafin harba na’urar kamar yadda aka tsara.

Ta kara da cewa, yanzu haka, kayayyaki a cibiyar harba kumbunan suna cikin yanayi mai kyau, kuma tuni shirye-shiryen harba na’urar suka kankama. (Fa’iza Mustapha)