logo

HAUSA

Hukumar EFCC ta Nijeriya ta fara binciken dakatacciyar minista da ake zargi da badakalar kudi

2024-01-10 10:36:34 CMG Hausa

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriya EFCC, ta fara gudanar da bincike kan Betta Edu, ministar kula da ayyukan jin kai da yaki da fatara da aka dakatar biyo bayan wata badakalar kudi da ake zargin ofishinta da aiwatarwa.

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ne ya dakatar da Betta Edu a ranar Litinin, domin ba hukumar EFCC damar gudanar da cikakken bincike.

Kafafen yada labarai na kasar sun ruwaito cewa, dakatacciyar ministar ta isa hedkwatar hukumar EFCC da safiyar jiya Talata, domin amsa tambayoyin masu aiwatar da binciken.

Betta Edu na shan suka daga al’ummar kasar bayan zargin da aka yi mata na bayar da umarnin tura wasu kudi naira miliyan 585.2 da za a rabawa masu rauni a kasar, zuwa wani asusun bankin ma’aikacin gwamnati. (Fa’iza Mustapha)