logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya amsa wasikar mai sada zumunta ta jihar Iowa ta Amurka Sarah D. Lande

2024-01-10 14:11:27 CMG Hausa

A ranar 4 ga wannan wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar mai sada zumunta ta jihar Iowa ta Amurka Sarah D. Lande, inda ya jaddada cewa, makomar dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka tana da nasaba da matasan kasashen biyu. Yana fatan karin matasa da yaran kasar Amurka za su kawo ziyara kasar Sin, da bude idanunsu da ganin kasar Sin na hakika a dukkan fannoni, kana za su kara kafa gadar sada zumunta a tsakanin jama’ar kasashen biyu.

A kwanakin baya, mai sada zumunta ta jihar Iowa ta kasar Amurka Sarah D. Lande ta aika wasika ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, inda ta bayyana cewa, jawabin shugaba Xi a gun liyafar maraba da kungiyar hadin gwiwa ta sada zumunta ta kasar Amurka ta gudanar ya burge jama’a sosai, inda aka bayyana cewa za a gayyaci matasa da yara na kasar Amurka dubu 50 su zo kasar Sin domin yin mu’amala da karatu. Tana mai fatan makarantar sakandare ta Muscatine za ta shiga wannan shiri. Ta kara da cewa, a matsayin manyan kasashen duniya, ya kamata Amurka da Sin su yi hadin gwiwa wajen daidaita matsalolin sauyin yanayi, da tsaron hatsi, da miyagun kwayoyi, da rikici a yankuna da sauransu, tana cewa hakan ne za a amfanawa dan Adam baki daya. (Zainab Zhang)