logo

HAUSA

Musanyar ziyarar tawagar matasan Sin da Amurka masu wasan kwallon tebur na ci gaba da rubuta babin sada zumunta na "Diflomasiyyar wasan"

2024-01-09 20:56:51 CMG HAUSA

 

Yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta amsa tambayoyin da aka yi mata a gun taron manema labarai cewa, bayan ganawar da shugabannin kasashen Sin da Amurka suka yi a birnin San Francisco, an gudanar da mu'amalar sada zumunta tsakanin jami'o'in kasashen biyu, inda a baya-bayan nan, tawagar ‘yan wasan kwallon tebur ta jami'ar Peking ta ziyarci Amurka, a hannun guda kuma tawagar ‘yan wasan kwallon tebur ta jami'ar Virginia ta ziyarci kasar Sin.

Game da wannan batu, Mao Ning ta bayyana cewa, ziyarar da aka yi tsakanin tawagogin ‘yan wasan kwallon tebur na matasan kasashen Sin da Amurka, ta ci gaba da zama wani babi na sada zumunta na "diflomasiyyar wasan kwallon tebur" da cusa sabon karfin mu'amala tsakanin al’ummomin Sin da Amurka. Makomar huldar kasashen biyu ya danganta da cudanyar al’ummun biyu, kuma yana da tushe daga jama’a, ban da wannan kuma matasa na taka rawa matuka a wannan fanni.

Mao Ning ta kara da cewa, Sin na fatan kara hadin kai da Amurka don tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, a yayin ganawarsu a San Francisco, ta yadda za a ci gaba da zurfafa dankon zumunci tsakanin jama’ar kasashen biyu. (Amina Xu)