logo

HAUSA

Sin na sa ran samun tafiye tafiye miliyan 80 na fasinjojin da za su yi bulaguro ta jiragen sama yayin bikin bazara dake tafe

2024-01-09 10:35:10 CMG Hausa

Hukumar kula da sufurin jiragen saman fasinjoji ta kasar Sin, ta ce bangaren na sa ran samun tafiye-tafiye miliyan 80 na fasinjoji yayin bikin sabuwar shekarar gargajiya ta kasar dake tafe.

A cewar hukumar, adadin ya kai karuwar kaso 44.9 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara, kuma ya kai karuwar kaso 9.8 akan wanda aka samu a makamancin lokacin a shekarar 2019.

Wata jami’ar hukumar mai suna Liang Nan, ta bayyana cewa, a bana, wannan lokaci na tafiye-tafiye zai kai har tsawon kwanaki 40, inda zai fara daga ranar 26 ga watan Junairu zuwa 5 ga watan Maris.

Ta kara da cewa, bangaren na sa ran gudanar da tafiye-tafiye miliyan 2 a kullum a matsakaicin mataki a lokacin, tare da tashin jirage kimanin 16,500 a kullum a matsakaicin mataki. (Fa’iza Mustapha)