logo

HAUSA

Kasar Sin za ta gudanar da aikin hatsi mai inganci ta hanyar ayyuka guda 6

2024-01-09 16:19:42 CMG Hausa

A shekarar bana, kasar Sin za ta gudanar da aikin samar da hatsi mai inganci ta hanyar ayyuka guda 6 da suka hada da gaggauta gina manyan sansanoni da kamfanoni da masana’antu da kuma dakunan ajiye abinci maras gurbata muhalli domin aikin noma na zamani.

Yayin taro kan aiki da aka gudanar a ranar 8 zuwa ranar 9 ga wata kan ajiye abinci da kayayyaki na kasar Sin, shugaban hukumar ajiye abinci da kayayyaki ta kasar Sin, Liu Huanxin, ya bayyana cewa, an samu karin inganci a sana’ar samar da abinci a shekarar bara ta hanyar gudanar da aikin hatsi mai inganci. An yi kiyasin cewa, kudaden shiga da masanan’antun abinci suka samu a shekarar bara ya kai yuan triliyan 4.3, wanda ya karu da kashi 7 cikin dari bisa makamancin lokacin a bara. (Safiyah Ma)