logo

HAUSA

Sin za ta fitar da sabon tsarin tafiyar da layin dogo

2024-01-08 19:26:08 CMG Hausa

Hukumar kula da jiragen kasa ta kasar Sin, ta bayyana cewa, Sin za ta fara aiki da wani sabon shirin gudanar da layin dogo, wanda zai fara aiki daga ranar 10 ga watan Janairun shekarar 2024, da nufin inganta karfin jigilar kayayyaki da fasinjoji.

A cewar hukumar, karkashin sabon shirin, za a kara sabbin jiragen kasa na fasinja guda 233 a fadin kasar, wanda ya kawo jimillar adadinsu zuwa 11,149.

Jimillar jiragen kasa na jigilar kayayyaki guda 22,264 ne za su rika aiki a fadin kasar, bayan shirin ya fara aiki, karuwar jirage 40, idan aka kwatanta da tsarin da ake amfani da shi a halin yanzu. (Ibrahim)