logo

HAUSA

Yawan masu bude ido da suka ziyarci yankin Xizang ta Sin ya kai sabon matsayi a shekarar 2023

2024-01-08 14:01:07 CMG Hausa

Shugaban gwamnatin jihar Xizang mai cin gashin kanta, Yan Jinhai ya bayyana cewa, a shekarar 2023, gaba daya mutane miliyan 55 ne suka je yawon shakatawa a jihar. Lamarin da ya samar da kudin shiga Yuan biliyan 65 kwatankwacin dallar Amurka biliyan 9 ga jihar. Adadin da ya kai matsayin koli a tarihin jihar a fannin yawon shakatawa.

Yan Jinhai ya bayyana hakan ne a cikin rahoton aikin gwamnati da aka gabatar a cikakken zaman taro karo na biyu na majalisar wakilan jama'ar jihar Xizang ta 12.

A shekarar 2024, jihar Xizang za ta yi amfani da albarkarun da Allah ya hore masa a fannin al’adu da yawon shakatawa da sauransu wajen kyautata ababen more rayuwa a fannin yawon shakatawa, da samar da wuraren yawon shakatawa masu kyau sama da guda 10 a jihar, da kuma kyautata yanayin kauyuka na musamman guda 15.

Haka kuma, an yi has ashen cewa, a shekarar 2023, GDPn jihar Xizang, wato jihar Tibet za ta zarce Yuan biliyan 230, adadin da ya karu da kaso 9 bisa 100, yawan kudin kashewa na kowane mutum zai kai Yuan dubu 60. Kana, yawan kudin kashewa na kowane mazauna biranen jihar, zai zarce Yuan dubu 50, adadin da ya karu da kaso 6.5 bisa dari, yayin da kudin kashewa na kowane mazauna kauyuka zai zarce Yuan dubu 20, adadin da ya karu da kaso 10 bisa dari. Haka kuma saurin karuwar manyan ma’aunan tattalin arziki da suka hada da jarin da aka zuba a fannin kadarori, da jimillar kayayyakin yau da kullum da aka sayar, da kuma jimillar kayayyakin shiga da fice da sauransu, yana kan gaba a fadin kasar Sin. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)