logo

HAUSA

Xi ya jaddada bukatar samun cikakkiyar nasara wajen yaki da cin hanci da rashawa

2024-01-08 19:35:01 CMG Hausa

Babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a ci gaba da yin gyare-gyare a jam'iyyar, da samun nasara a yakin da ake yi da matsalar cin hanci da rashawa.

Xi, wanda kuma shi ne shugaban kasar Sin, kuma shugaban rundunar sojojin kasar, ya bayyana haka ne, yayin da yake jawabi ga cikakken zaman taro karo na uku na kwamitin kolin ladabtarwa na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20. (Ibrahim)