logo

HAUSA

Ma’aikatar Kasuwanci: kasar Sin tana da kyawawan sharuddan jawo jarin waje

2024-01-08 14:00:29 CMG Hausa

A yayin taron tattaunawa kan harkokin tattalin arzikin kasar Sin da aka shirya a yau a nan Beijing, wani jami’in ma’aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin ya bayyana cewa, har yanzu kasar Sin na da kyawawan sharuddan jawo jarin waje.

Darektan sashen kula da harkokin zuba jari na ketare na ma’aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin Zhu Bing ya bayyana cewa, bisa hasashen da aka yi, an ce, ya zuwa karshen shekarar 2023, gudummawar da kasar Sin ta bayar a fannin karuwar tattalin arzikin kasashen duniya za ta kai kashe 1 bisa uku, kuma kasar za ta ci gaba da kasancewa babban karfin dake inganta karuwar tattalin arzikin duniya, kuma, tattalin arzikin kasar Sin zai bunkasa cikin yanayin zaman karko. Ya kara da cewa, kamfanonin kasashen ketare suna mai da hankali kan manyan kasuwannin kasar Sin, da karfinta na yin kirkire-kirkire da sauransu.

A nan gaba kuma, Zhu Bing ya bayyana cewa, kamfanonin kasashen ketare suna da kwarin gwiwa game da kasuwannin kasar Sin, za su ci gaba da zuba jari a kasar Sin, sabo da kasuwannin Sin na da makoma mai haske. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)