logo

HAUSA

Sin ta yanke shawarar kakaba takunkumi ga kamfanonin tsaron Amurka guda biyar

2024-01-07 15:56:25 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ta yanke shawarar sanya takunkumi ga kamfanonin tsaron Amurka guda biyar.

A baya-bayan nan ne Amurka ta sanar da sayar wa yankin Taiwan na kasar Sin sabbin makamai tare da sanya wa 'yan kasuwa da wasu Sinawa takunkumi, bisa wasu dalilai marasa tushe. Kakakin ya sanar da matakin ne lokacin da aka tambaye shi game da matakan da Sin ke dauka kan wannan batu.

A cewar kakakin, yadda Amurka ta sayarwa yankin Taiwan na kasar Sin makamai, ya saba wa manufar kasar Sin daya tak a duniya, da kuma sanarwoyi guda uku da sassan biyu suka sanyawa hannu, musamman ma sanarwar hadin gwiwa ta ranar 17 ga watan Agustan shekarar 1982, da takunkumin da Amurka ta kakaba wa kamfanoni da daidaikun Sinawa bisa ka'idojin karya daban-daban, kuma suna yin illa sosai ga diyaucin da ma moriyar tsaron kasar.

Bugu da kari, cinikin makamai da takunkumin da Amurka ta kakaba ba bisa ka'ida ba, sun kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan, da keta 'yanci da halastattun hakkoki da muradun kamfanoni da daidaikun jama’a. Don haka, kasar Sin tana kakkausar suka da nuna adawa da hakan, ta kuma gabatar da kokenta ga kasar Amurka.

Ya bayyana cewa, a matsayin mayar da martani ga wadannan munanan ayyuka na kuskure da Amurka ta dauka, kuma bisa ga dokar yaki da sanya takunkumai na kasar Sin, kasar Sin ta yanke shawarar kakaba takunkumi ga kamfanonin tsaron Amurka guda biyar, wato BAE Systems Land and Armament,da Alliant Techsystems Operation, da Aero Vironment, da ViaSat, da kuma Data Link Solutions.(Ibrahim)