logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara daukar matakai wajen rage farashin kayan abinci a kasar

2024-01-06 14:40:10 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa, yanzu haka tana aikin tabbatar da ganin ’yan Najeriya na samun kayan abinci a kan farashi mai sauki kuma a wadace.

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tunibu ne ya tabbatar da hakan a fadarsa dake birnin Abuja lokacin da ya gana da gwamnonin jihohin Gombe da Niger inda suka tattauna a kan yadda za a samu hadin gwiwa da jihohin wajen wadata kasa da abinci.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce, jihohin Niger da Gombe suna daya daga cikin jihohin da gwamnatin tarayyar ta ware wajen samar da cibiyar sarrafa kayan amfanin gona, inda ya ce domin tabbatar da wannan aniya, gwamnati ta tsara noma filin noma mai fadin hekta dubu dari 5 a sassan kasar, daga cikin kuma kayan gonar da za a noma sun hada da masara, shinkafa, gyero da sauran kayan abinci.

“Domin tabbatar da wadatuwa abinici, a karshen shekarar bara ta 2023 mun kaddamar da shirin noman rani a filin mai fadin hekta 120,000 a jihar Jigawa.”

Da yake ganawa da manema manema labarai jim kadan da kammala taron, gwamnan jihar Gombe Alhaji Inuwa Yahaya ya ce, “Mun samar da rukunin masana’antun sarrafa kayan amfanin gonar da ake nomawa a jihar Gombe, ina da yakinin cewa muddin sauran jihohi za su dauki irin matakan da muka dauka tabbas akwai yiwuwar samun nasarar wannan manufa ta gwamnatin tarayya.”

Shi kuwa gwamnan jihar Niger Umar Muhammad Bago yabawa ya yi da yunkurin gwamnatin tarayyar na noma hekta dubu dari 5 a bana, “kuma jihar Niger tana cikin jihohin da za a samar da irin wadannan filaye na noma, duk da haka mu ma mun ci burin samar da karin hekta dubu dari 5, kari a kan wanda gwamnatin tarayyar ta yanke shawarar nomawa a jihar.” (Garba Abdullahi Bagwai)