logo

HAUSA

Majalisar Gudanarwar Sin Ta Yi Kira Da A Kara Bunkasa Tsarin Kula Da Tsoffi

2024-01-06 15:56:22 CMG Hausa

Majalisar gudanarwar kasar Sin ta gudanar da wani taron zartaswa, don nazarin ci gaban da aka samu a bangaren dake shafar tsoffi a cikin al’umma.

Taron wanda firaministan kasar Li Qiang ya jagoranta, ya jaddada cewa, fadada wannan bangare na tattalin arziki, wani muhimmin mataki ne na mayar da kula da rayuwar da jama'ar da suka tsufa, da sa kaimi ga samun bunkasuwa mai inganci da za su amfana a yanzu da kuma nan gaba.

A cewar taron, ya zama wajibi gwamnati ta sauke nauyin da aka rataya a wuyanta na biyan bukatun yau da kullum, da karfafa tsarin samar da ababen more rayuwa ga tsofaffi, da kara samar da muhimman ababen more rayuwa.

Ya jaddada muhimmancin amfani da hanyoyin kasuwa, da cikakken amfani da rawar da kungiyoyin 'yan kasuwa da na jama'a daban daban suke takawa, da kuma biyan bukatun rukunonin tsoffi daban daban.

Taron ya bayyana cewa, ya zama tilas a ci gaba da inganta manufofi da matakan da suka dace, tare da mai da hankali kan magance wasu muhimman bukatu, irinsu gidajen kula da tsoffi, jiyya, da kula da lafiyar tsoffi.(Ibrahim)