logo

HAUSA

Sin ta fitar da shirin bunkasa cin gajiya daga bayanai ko data

2024-01-05 09:38:13 CMG Hausa

Kasar Sin ta fitar da shirin aiki na shekaru 3, da nufin bunkasa cin gajiya daga bayanai na ainihi ko data, wajen ingiza samar da hajoji, tare da mayar da bayanai na data a matsayin jigon bunkasa tattalin arziki, da raya zamantakewar al’umma.

Karkashin shirin, wanda sassan hukumomin kasar 17, ciki har da hukumar data ta kasar Sin ko NDA suka wallafa, za a rika amfani da bayanai na data wajen bunkasa sassa 12, kama daga ingiza fannin samar da hajoji, da hada hadar cinikayya, zuwa kirkire-kirkiren fasahohi, da bunkasa ci gaba ta amfani da makamashi marasa dumama yanayi.

Bisa sabon shirin, cikin shekaru 3 tun daga shekarar nan ta 2024, Sin za ta kara azamar bunkasa amfani da data, da tabbatar da samar da ingantacciyar data, da kyautata yanayin musayar data, da karfafa tsaron ta.

An kafa hukumar NDA ne a watan Oktoban shekarar 2023, a wani bangare na bunkasa aniyar Sin ta ingiza tsare-tsare, da gina Sin mai aiki da fasahohin sadarwa ko "Digital China,", ciki har da fannonin tattalin arziki da zamantakewa na dijital.  (Saminu Alhassan)