logo

HAUSA

Sin Ta Bukaci Yin Shawarwari Da Tuntubar Juna Don Warware Matsalar Zirin Koriya

2024-01-05 19:59:40 CMG Hausa

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, kasar Sin na ba da shawarar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Koriya, da warware matsalar zirin ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna.

Mai magana da yawun ma'aikatar Wang Wenbin ne ya bayyana hakan, a yayin taron manema labarai na yau da kullum Jumma’ar, lokacin da yake karin haske dangane da halin da ake ciki a yankin.

Wang ya bayyana cewa, halin da ake ciki na baya-bayan nan a mashigin tekun na ci gaba da dagulewa, kasar Sin na fatan dukkan bangarorin da abin ya shafa, za su kwantar da hankula da kai zuciya nesa, da kauracewa daukar matakan da za su kara tayar da hankula, don samar da yanayin sake dawo da shawarwari mai ma'ana.(Ibrahim)