logo

HAUSA

CMG Ya Gabatar Da Dandamali 4 Na Gudanar Da Shirin Talibijin Na Murnar Sabuwar Shekarar 2024 Bisa Kalandar Gargajiyar Kasar Sin

2024-01-04 21:27:26 CMG Hausa

Alhamis din nan ne, babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya gabatar da dandamali 4 na gudanar da shirin talibijin na murnar sabuwar shekarar 2024 bisa kalandar gargajiyar kasar Sin.

A dandamalin da ke birnin Shenyang na lardin Liaoning, da Changsha na lardin Hunan, da Xi'an na lardin Shaanxi da Kashgar na jihar Xinjiang, tare da babban dandamalin da ke birnin Beijing, za a nuna shirin talibijin na murnar sabuwar shekarar Loong bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, ga al’ummar Sinawa dake zaune a fadin duniya a jajibirin sabuwar shekarar bisa kalandar gargajiyar kasar Sin. (Ibrahim)