logo

HAUSA

Sin ta kalubalanci wasu kasashe su daina ayyukan da ba su dace ba

2024-01-04 20:31:45 CMG Hausa

Dangane da aikin sintiri na hadin gwiwa da kasashen Philippines da Amurka suka yi a baya-bayan nan a tekun kudancin kasar Sin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, kasashen biyu sun yi aikin soja a tekun kudancin kasar Sin don shaida karfinsu na soja, matakai da zai kawo illa ga kiyaye yanayin teku da tada rikici a tekun. Kasar Sin ta kalubalanci kasashen da abin ya shafa da su dakatar da ayyukan da ba su dace ba, da girmama kokarin kasashe da yankuna na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar Sin. Kasar Sin za ta ci gaba da kiyaye ikon mulkin kasa da cikakken yankinta da hakki da moriyarta ta teku, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. (Zainab)