logo

HAUSA

Sirrin Amurka na canja ra’ayoyin jama’a kan kasar Sin

2024-01-04 11:25:43 CMG Hausa

Kwanan baya, masanin Turai Jan Oberg ya bayyana cewa, kasar Amurka ta taba gabatar da wani daftari, wanda a cikinsa ta shawarci da a samar da kudade cikin shekaru 5 masu zuwa a jere, domin ba da horo ga ’yan jaridu, a fannin yada jita-jitar da za ta bata sunan kasar Sin. Kuma shaidun da aka gano sun bayyana cewa, wannan daftarin da Jan Oberg ya ambata ya yi daidai da “daftarin yin gasa bisa manyan tsare-tsare na shekarar 2021”, wanda kwamitin kula da harkokin kasashen waje na majalisar dattawa ta kasar Amurka ya zartas a watan Afrilu na shekarar 2021.

Daftarin ya ba da shawarar cewa, daga shekarar 2022 zuwa shekarar 2026, a kowace shekara, kasar Amurka za ta kebe dalar Amurka miliyan dari 3, wato gaba daya dalar Amurka biliyan 1 da miliyan dari 5 cikin wadannan shekaru biyar, domin yin amfani da su wajen rage tasirin da kasar Sin ta yi wa kasashen duniya.

Bisa wannan daftari, a kowace shekara za a kashe dalar Amurka miliyan dari 1, wajen tallafawar hukumar kual da kafofin watsa labarai ga kasashen duniya ta kasar Amurka, da dai sauran hukumomin da abin ya shafa, don su sa ido, da mayar da martani kan labaran da kasar Sin ke fitarwa. A sa’i daya kuma, hukumomin gwamnatin kasar Amurka za su talalfa da kuma horas da ’yan jaridu, domin taimaka musu wajen nazarin shirye-shirye masu nasaba da shawarar “Ziri daya da hanya daya”.

Haka kuma, sau da dama, an ambaci jihar Xinjiang ta kasar Sin cikin wannan daftari, inda ya bukaci kasar Amurka da ta tsoma baki cikin harkokin jihar Xinjiang ta kasar Sin.

Kasar Amurka ta dade tana daukai matakai a fannin canja ra’ayin jama’a, da na harkar soja, da kuma a fannin tattalin arziki da dai sauransu, domin kare kanta a matsayin babbar kasa daya tilo a duk fadin duniya.

Masana na ganin cewa, kasar Amurka tana fatan farfado da matakan yake-yake a fannin sauya ra’ayin jama’a, kamar yadda ta taba aikatawa a lokacin Yakin Cacar Baka, sai dai kuma matakan ba su dace da halin da muke ciki ba, kuma ba za ta cimma nasarar cutar da sauran kasashen duniya kan wannan harka ba. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)