logo

HAUSA

An tuhumi tsohon shugaban kasar Saliyo da laifin cin amanar kasa

2024-01-04 11:01:49 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Saliyo ta sanar da cewa, ana tuhumar tsohon shugaban kasar Ernest Bai Koroma, da laifin cin amanr kasa da sauran wasu laifuffuka saboda rawar da ya taka a yunkurin juyin mulki a kasar.

Cikin wata sanarwa, ma’aikatar yada labarai ta kasar ta bayyana cewa, tsohon shugaban kasar na fuskantar tuhume-tuhume 4 da suka hada da cin amanar kasa da rashin sanar da hukumomi game da yunkurin cin amanar kasa da sauran wasu laifuffuka 2 da suka shafi boye masu laifi. 

Sanarwar ta kara da cewa, Ernest Bai Koroma wanda ya rike ragamar shugabancin kasar daga 2007 zuwa 2018, na da lauyoyin dake kare shi. Haka kuma ta tabbatarwa al’umma cewa za ta rika sanar da su game da yadda shari’ar ke gudana.

A ranar 26 ga watan Nuwamban bara, wasu mutane dauke da makamai suka kutsa barakokin soji da wani gidan yari da sauran wasu wurare a Freetown, babban birnin kasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 20 a wani yunkuri da gwamnatin kasar ta ayyana a matsayin juyin mulki da bai yi nasara ba. (Fa’iza Mustapha)