logo

HAUSA

Shugabancin CPC Ya Saurari Rahotannin Aiki

2024-01-04 21:15:37 CMG Hausa

A yau ne zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya gudanar da wani taro domin sauraran rahotannin ayyuka.

Wadannan rahotannin sun fito ne daga zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da majalisar gudanarwar kasar, da kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, da kotun koli ta jama'ar kasar, da babbar hukumar gabatar da kararraki, da sakatariyar kwamitin kolin JKS.

Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin JKS, shi ne ya jagoranci taron, tare da gabatar da muhimmin jawabi.

Taron ya yi nuni da cewa, tun bayan babban taron wakilan JKS karo na 18 da aka gudanar a shekarar 2012, kwamitin kolin JKS ya kan saurari rahoton ayyuka na musamman a ko wace shekara, wanda wani muhimmin tsari ne na karfafa jagorancin jam'iyyar. Wannan tsari ya dace da jagorancin jam'iyyar da ma tsare-tsaren dukkan bangarori, da kiyaye hadin kan jam'iyyar da babban karfin jam’iyyar, da nuna fifikon tsarin gurguzu mai sigar kasar Sin.(Ibrahim)