logo

HAUSA

Sin ta kalubalanci kasar Amurka da ta daina takurawa daliban Sin dake karatu a Amurka bisa dalilin kiyaye tsaron kasa

2024-01-04 20:34:03 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, kasar Sin ta bukaci kasar Amurka da ta aiwatar da furucinta na maraba da daliban kasar Sin, da soke dokar nan mai lamba 10043 da ba ta dace ba, da kuma daina amfani da tsaron batun kasa a matsayin wani uzuri na dakile kasar Sin da takurawa daliban kasar dake karatu a Amurka, da tabbatar da hakkin masana da daliban Sin a kasar Amurka, don cika alkawarin da ta yi na goyon bayan saukaka mu’amalar al’adu da ma’aikata a tsakanin Sin da Amurka. (Zainab)