logo

HAUSA

Sin Za Ta Ci Gaba Da Kasancewa Wani Muhimmin Injin Din Kara Bunkasa Tattalin Arzikin Duniya

2024-01-04 20:05:10 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana Alhamis din nan, yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa game da hasashe kan tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2024 cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kasancewa wani muhimmin injin din ci gaban tattalin arzikin duniya a sabuwar shekara, da samar da tabbaci da ginshiki mai inganci ga tattalin arzikin duniya mai cike da rashin tabbas.

Wang Wenbin ya ce, a cikin shekarar da ta gabata, tattalin arzikin kasar Sin ya jure matsin lamba daga waje, ya ci gaba da farfadowa, tare da samun ci gaba mai inganci. Bayanai sun tabbatar da cewa, tushen tattalin arzikin kasar Sin, mai cike da kwanciyar hankali da inganci cikin dogon lokaci, bai sauya ba, kasashen duniya na kara amincewa da tattalin arzikin kasar Sin a wannan shekara. (Ibrahim).