logo

HAUSA

An ceto sama da bakin haure 17,000 daga gabar tekun Libya a 2023

2024-01-03 14:07:02 CMG Hausa

Hukumar kula da kaura ta duniya IOM, ta ce jimilar bakin haure 17,025 ne aka ceto tare da mayar da su Libya a shekarar 2023.

A cewar rahoton da hukumar IOM ta fitar jiya Talata, a makon da ya wuce kadai, bakin haure 1,234 ne aka ceto tare da mayar da su Libya.

Har ila yau a shekarar 2023, wasu kimanin 974 sun mutu yayin da 1,372 suka bace a cikin teku Bahar Rum a kan hanyarsu ta shiga Turai daga Libya.

Saboda rashin tsaro da rikici a Libya tun bayan hambarar da gwamnatin marigayi Muammar Gaddafi a shekarra 2011, bakin haure da dama, galibinsu ‘yan Afrika sun zabi bin tekun Bahar Rum domin shiga Turai. (Fa’iza Mustapha)