logo

HAUSA

Harbin Kasar Sin Ya Samu Bunkasuwar Yawon Shakatawa A Lokacin Hutun Murnar Sabuwar Shekara

2024-01-03 21:10:41 CMG Hausa

Harbin, babban birnin lardin Heilongjiang na arewa maso gabashin kasar Sin, ya yi maraba da kusan maziyarta miliyan 3.05, inda aka samu kudin shiga da yawansa ya kai kudin Sin RMB yuan biliyan 5.91 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 832.39 a lokacin hutun kwanaki uku na murnar sabuwar shekara, wanda ya kare a ranar Litinin.

Duk adadin masu yawon bude ido da adadin kudaden shiga na yawon shakatawa sun zarce alkaluman shekarar 2019, wadanda suka kafa tarihi.

Bayanai daga sashen kasuwanci na birnin sun nuna wani gagarumin ci gaba da ya kai kashi 129.4 cikin dari a sassan dakunan kwana da na abinci a lokacin hutun.

Don jawo hankalin masu yawon bude ido da habaka hidimomi gaba daya, Harbin ya kaddamar da jerin ayyuka, da suka hada da wasannin nishadi kai tsaye a jajiberen sabuwar shekara, da wasan wuta, da wuraren shakatawa, da nune-nunen al’adun gargajiya da shagalin kade-kade da wake-wake. (Yahaya)