logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya sanya hannu kan dokar kasafin kudin shekara ta 2024

2024-01-02 09:41:14 CMG Hausa

A jiya Litinin 1 ga wata, a fadarsa dake Abuja, shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan kudurin dokar kasafin kudin shekara ta 2024, inda ya tabbatar da cewa, zai yi bakin kokarin ganin an aiwatar da abubuwan dake kunshe cikin kasafin kudi a kan lokacin da aka tsara tare da ganin cewa zaton alherin da jama’a ke yi a kan kasafin sun tabbata.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

A lokacin da yake jawabi bayan kammala sanya hannu, shugaba Tinubu ya shaidawa ’yan Najeriya cewa gwamnati za ta bi sau da kafa wajen sanya idanu a kan ayyukan da za a gudanar karkashin kasafin kudin.

“A yau muna da kasafin kudin da ya kai naira tiriliyon 28.7 wanda ya hada da karin naira tiriliyon 1.2 a kan ainihin adadin da na turawa majalissa. Ina matukar godiya ga ’yan majalissar kasa bisa duba a tsanake da gyare-gyaren da suka yi a kan kasafin kudi. Wannan ya nuna cewa, kawai kyakkyawar fahimta tsakanin majalissa da bangaren zartaswar gwamnati, ina fatan hakan zai cigaba da dorewa.”

Shugaba Tinubu ya ce, a jawaban da ya sha yi a baya, ya bayyana kasafin na bana a matsayi na sabunta kyakkyawan fata ga kasa.

Ya ci gaba da cewa, kasafin kudin na 2024 ya karkata kan kara adadin kudaden da ake kashewa wajen manya ayyuka musamman ma a bangarorin da gwamnati ta dora mahimmanci a kansu, sannan kuma an rage kudaden da za a kashe wajen ayyukan yau da kullum. Ha’ila yau kasafin kudin na 2024 ya rage gibin da ake samu daga kaso 6.11 zuwa kaso 3.88. Wannan kamar yadda shugaban ya fada babbar nasara ce sosai. (Garba Abdullahi Bagwai)