logo

HAUSA

Jawabin shugaba Xi na murnar sabuwar shekara ya burge jama’a sosai

2024-01-02 20:47:20 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, gabanin karatowar sabuwar shekara wato shekarar 2024, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da jawabin murnar sabuwar shekarar, inda ya waiwayi nasarorin da Sin ta samu a shekarar 2023, da bayyana kyakkyawar makomar jama’ar kasar Sin wajen yin kokarin neman cimma burinsu, kana ya bayyana fatan Sin na yin kokari tare da kasa da kasa don kirkiro kyakkyawar makoma tare, jawabin ya burge jama’a sosai.

Game da wannan jawabi, Wang Wenbin ya bayyana cewa, a cikin shekarar 2023, kasar Sin ta cimma nasarar gudanar da taron koli na Sin da kasashen tsakiyar Asiya, da dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar kasashen da ke raya shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya karo na uku, gasar wasannin motsa jiki ta daliban jami’o’i ta duniya ta Chengdu, da gasar wasannin motsa jiki ta Asiya ta Hangzhou, Sin ta yi kokari tare da bangarori daban daban wajen yin kiran samun zaman lafiya da bunkasuwa da kuma kiyaye yin hadin gwiwa don samun moriyar juna. Shugaba Xi ya kai ziyarar aiki a kasashen waje sau hudu, da halartar tarurukan kasa da kasa, da ganawa da tsofaffin abokai da sabbin abokai, da more ra’ayoyin Sin, da cimma daidaito da juna, da kuma nunawa bangarori daban daban yakinin Sin wajen tinkarar kalubale da mawuyacin hali tare. Bangarori daban daban sun gano cewa, Sin ta raya kanta, kana tana son yin kokari tare da kasashen duniya wajen samun bunkasuwa tare. (Zainab)