logo

HAUSA

Sin ta kaddamar da kidaya ta kasa a fannin tattalin arziki

2024-01-02 10:30:33 CMG Hausa

A jiya Litinin ne gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da kidayar kasa baki daya a fannin tattalin arziki. Karkashin shirin na kidaya, jami’ai miliyan 2.1 za su tattara bayanai, da rajistar mamallaka sana’o’i da rukunonin al’umma, wadanda aka shata karkashin yankunan tattara bayanai miliyan 1.16.

A cewar hukumar kididdiga ta kasar Sin NBS, za a gudanar da kidayar ne cikin watanni hudu. Ana kuma gudanar da wannan kidaya ne bayan duk shekaru 5.

A watanni 6 na karshen shekarar bara ne NBS ta gudanar da ayyukan shirya tunkarar kidayar, wadda kuma a yanzu ake gudanar da ita tun daga farkon wannan shekara ta 2024. An tsara aiwatar da rajistar masu sana’o’i a wuraren da suke, da tantance ingancin bayanan da aka tattara, tare da fitar da muhimman alkaluman bayanan.

A cewar shugaban hukumar ta NBS Kang Yi, kidayar ta wannan karo wadda ita ce karo na 5, za ta nazarci matsayin ci gaban tattalin arziki, tare da fayyace nagartar masana’antun Sin na kere-kere, da na bayar da hidimomi. (Saminu Alhassan)