logo

HAUSA

Goron Barka Da Shiga Sabuwar Shekarar 2024 Daga Jawabin Shugaban kasar Sin

2024-01-01 20:48:51 CMG Hausa

Daga Abdulrazaq Yahuza


Kwarin gwiwar da shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya bai wa al'ummar kasarsa a jawabin da ya gabatar na maraba da sabuwar shekarar miladiyya ta 2024, ya nuna irin yadda Sinawa da shugabanninsu suka zama tsintsiya madaurinki daya da tara karfi wuri guda wajen ciyar da kasarsu gaba.

Kamar yadda shugaban kasar ya nuna, kowa ba a raina kokarin da ya yi ba wajen bayar da gudunmawa ga samun nasarar abubuwan da kasar ta cimmawa a shekarar 2023. “Dukkanku, tun daga manoma a gonaki zuwa ma'aikata a kan benayen masana'antu, daga 'yan kasuwa zuwa ma'aikatan da ke gadin kasarmu--hakika, mutane daga kowane bangare na rayuwa - kun yi kokarinku. Kowane dan kasar Sin ya ba da gudummawa mai ban mamaki! Har kullum al'ummar Sinawa, abin dogara ne wajen jure wahalhalu.”

Ga duk wanda ya san Sinawa, ya san mutane ne masu aiki tukuru da nuna kishin kasa. Kamar yadda Shugaba Xi ya ayyana, duk da cewa, shekarar 2023 ta zo da ibtila'i kamar ambaliyar ruwa da girgizar kasa, amma kuma akwai abubuwa da aka samu nasara a kansu a zahiri, “za mu tuna wannan shekarar a matsayin daya daga cikin shekarun aiki tukuru da juriyar hakuri. Daga yanzu, muna da kwarin gwiwar gaba za ta fi kyau.”

A shekarar da aka yi ban kwana da ita, kasar Sin ta samu ci gaba mai inganci, inda aka bude wani sabon babi na farfado da yankunan karkara da yankin arewa maso gabashin kasar. Saurin ci gaban sabon yankin Xiong’an ya wuce yadda ake tsammani, kuma yankin tattalin arziki na kogin Yangtze ya bunkasa yayin da babban yankin Greater Bay na Guangdong, Hong Kong da Macao ya ba da jagora wajen samun ci gaba. Kasar Sin ta kara karfin tattalin arzikinta duk da matsaloli da dama da aka fuskanta.

Wani abu mai muhimmanci kan ci gaban Sin da shugaba Xi ya tabo a jawabin nasa shi ne batun kirkire-kirkiren fasaha wanda ya ba da misali da ci gaban da aka samu wajen fara sayar da dankareren sabon jirgin saman da kasar ta kera na C919, sannan babban jirgin ruwan da kasar ta kera ya kammala balaguron gwaji, kana 'yan sama jannati na Shenzhou na ci gaba da binciken da suke yi a sararin samaniya. Bugu da kari yadda kayan da Sin ke kerawa da ake ya yi kamar sabbin wayoyin hannu na zamani, motoci masu amfani da sabon makamashi manuniya ce a kan kwarewar masana'antun kasar.

Irin wannan ci gaba da Sin ke samu ba abin mamaki ba ne ga duk mai bibiyar tarihinta, domin kasa ce da take da tsari na wayewa tun fil azal, kuma ba ta yarda ta sauka daga kan layi ba. Kayan tarihin da aka gano a yankin Liangzhu da Erlitou sun kara fayyace abubuwa da yawa game da wayewar kasar Sin wanda Shugaba Xi ya ce shi ne sirrin kwarin gwiwarsu.

Kasancewar Sin kasa ta biyu a duniya wajen ci gaban tattalin arziki, Shugaba Xi ya ce ta sauke nauyin dake wuyanta. Ta gudanar da tarurruka daban-daban na hadin gwiwa da difilomasiyya a yankin Asiya, Afirka da sauran sassan duniya.

Kasar ta sha nanata bukatar kawo karshen mummunan yakin da ake gwabzawa a yankin Gaza tsakanin Hamas da Isra’ila ba kawai da fatar baki ba, amma a aikace kamar yadda ta rika kada kuri'a kan haka a zauren Majalisar Dinkin Duniya. Haka nan, ziyarar da Shugaba Xi ya kai Amurka kwanan baya da yadda manya da hamshakan Amurkawa suka rika kai ziyara Beijing a shekarar 2023, ya nuna aniyar kasar ta samar da duniya mai cike da zaman lafiya da cin moriyar juna. Ina iya tunawa, Shugaba Xi ya ce bai kamata gasa da juna ta fuskar ci gaba ta rikide ta zama kiyayya ba, a ganawarsa da Shugaba Joe Biden a birnin San Francisco.

Da yake Sin na cika shekara 75 da kafuwa a matsayin Jamhuriya a sabuwar shekarar da aka shiga, burin da Shugaba Xi ya bayyana a jawabinsa na samar da ingantacciyar rayuwa ga al’ummar kasa ta yadda yaran kasar za su samu ingantaccen ilimi, matasa su samu damar gudanar da sana'o'insu da samun nasarar abubuwan da suke fatan zama a rayuwa, da kula da dattawa da sauran harkoki da za su kyautata rayuwar al'umma, ya zama babban albishir ba ga Sinawa ba kadai har da sauran kawayenta musamman na Afirka da take taimakonsu su tsaya da kafafunsu.